Tambayoyin da ake yawan yi (FAQS)

Saboda me zan yi amfani da allevent.ng don taruka na? muna dauke maka wahalar zuwa bainar jama;a don sayarwa ko sayen tikiti don kana iya yin haka a dokinka a kowane lokaci. Hanya ce mai sauki ta sanar da tarukanka, sayarwa kao sayen tikiti na zuwa taruka/biki. Allevents.ng na samar da yanayi da kasuwar da ke hada masu tallar taruka / biki/ ta intanet da al’umma ta wurin rage kashe kudi tare da samar da harkar samun tikiti mai inganci na shiga taruka na musamman a Najeriya.

TA YAYA ZAN FARA?

Da farko ka shiga www.allevents.ng sai ka danna “login” ka shiga ta shafin sadarwarka ko ta imel dinka. Za a turo maka kafa ta tabbatarwa ta imel dinka sai ka shiga don ka cike bayananka.

TA YAYA ZAN SAYI TIKITI?

Fara da neman taro da kake so ta zabin da muka samar a dandalin intanet dinmu. Kama iya faraway da zabin yare wadda zai kai kai shiyya kai tsaye, ko kuma ka shigar da sunan taron ko birnin a wajen bincike na shafin. Shiga taron inda zai kai ka bangaren tikiti, inda za a bayyana kudi shiga taron. Kana iya zaben hanyar kudi da zarar ka samar da bayanan da ake bukata.

TA YAYA ZAN SAYAR DA TIKITI?

Shiga shafinka, kuma idan baka da account da mu, ka yi rajista ta shafin sadarwaka ko imel.

Tabbatar da kafar da aka turo ta imel dinka, zabi “sell ticket” daga saman shafinka sannan ka shigar da taro, cike bayanan taron kuma ka sanya farashin tikiti.

Za a sanya taronka kai tsaye bayan an duba an kuma tamntance . wannan na iya daukan kasa da monti 30 lokacin aiki (8:00 zuwa 17:00) ko kuma fiye idan aka sanya taron tsakanin 18:00 zuwa 17:00.

Sai dai idan ana bukatar Karin bayani game da taronka, zamu tuntubeka kafin mu sanya taron kai tsaye.

Kai ma kana iya tuntubanmu a selltickets@allevent.ng.

TA YAYA ZAN TALLATA TARONA?

Shiga cikin shafinka kuma idan baka da account da mu sai ka bude wani ta wurin shiga ta shafin sadarwaka ko imel. Tabbatar da kafar (link) da aka turo ma ta imel dinka, zabi, “manage events” daga saman shafinka, daga nan sai ka sanya taronka, cike bayanan taron ka zabi tsawon lokacin da kake so a tallata taron kafin ranar taron.

Idan kuma kana so ne ka tallata taron da ke cikin shafinmu ne, sai ka shiga shafinka ka zabi a promotemyevents@allevents.ng

TA YAYA ZAN KARBI TIKITI NA?

Za a tura ma bayanan tikitinka ta kafar da ka zaba (imel ko waya) lokacin biya. Sai dai ana bukatar shaidar biyan kudi (receipt) ta kafar da ka zaba a lokacin da kake biyan kudin.

INA DA TIKITIN DA NA GURZA (PRINT) DAGA INTANET, ANA LA’AKARI DAS HI WAJEN SHIGA TARON?

Ana anfani da tikitin da aka tura ta intanet ko kuma wanda aka gurza (print) wajen shiga. Ka tabbata ka adana shi, kuma dukkan bayanan tikitin ba zai yi wuyan samu ba – ba za a amince da tikitin da ba za a iya karantawa ba.

NA TURA TARO AMMA BAN GAN SHI BA. ME YA SA.  

Kana iya bibiyar tarukanka ta wurin shiga shafinka ka kuma danna “manage events”. Jerin tarukan da ka tura zai kasance karkashin “your events”. Kana iya tantance matsayin taronka ta wurin shiga shafi inda zaka iya jiran amincewa da shi.

Domin ga al’amuraranka a allevents.ng ana nazarin duk tarukan da aka tura don bada kariya daga damfara ko coge. Ta wurin tantancewa daga admin din mu, abib da ka tura na iya daukan minti talatin lokacin aiki, (08:00 zuwa 17:00) kafin a daura shi kai tsaye. Sai dai yana iaya wuce haka idan aka tura taron tsakanin 18:00 zuwa 07:00.

Idan bayan awa 24 baka ga   taronka ba, sai ka duba imel din da ka bamu ka kuma sake gwada turawarko kuma ka tuntubemu a support@allevents.ng.

TA YAYA ZAN SANI KO AN DAGE TARON DA NA BIYA, KO AN CANZA LOKACI KO KUMA AN SOKE SHI?

Idan aka dage taron da ka biya, ko an canza lokaci ko an soke shi gaba daya zamu tura maka sanarwa ta imel ko lambar da ka ba mu. Zamu kuma baka Karin bayani kan sabbin bayanai game da tarukan. Saboda haka  ka sanar da mu da wuri.

ME ZAI FARU IDAN AKA SOKE TARONA?

Idan aka  so ke ko dage taron da ka biya kada ka damu zamu mayar maka da kudinka ta wurin masu shirya taron ko masu tallata taron.

Zamu kuma maka yadda zaka yi a mayar maka da kudinka. Sai dai hakan zai dan dauki lokaci saboda batun gudanarwa da tabbatar da tikitin. Yana kuma da mamahimmanci a ce kana da shaidar tikitinka na intanet. Idan kuma ka canza imel ko lambar wayarka sai ka sanar da mu da wuri.

TA YAYA ZAN TABBATAR DA SAYEN TIKITINA BAYAN NA BIYA?

Muna shiga “complete payment” da zarar mun karbi kudin tikitin da ka bukata. Dukkan sayayyan da aka kamala zai fitar da tikiti na musamman wadda zamu tura ta imel dinka ko wayarka. Idan baka samu tikiti a lokacin da ka saya ba, bukatarka bata shiga ba. Wani lokaci biyan kudi ta banki yana daukan sa ‘o’i kafin ya shiga. Zamu karfafa maka gwiwa ka sake gwadawa har sai bukatarka ta shiga, kuma ka karbi tikiti ta intanet na zuwa taronka a matsayin tabbatarwar bukatarka.

BAYANAN  KATI NA BA SA CIKIN HADARI A WURINKU?

Kwarai, muna anfani da ‘secure socket layer’ (SSL) technology wata fasaha ce da ke samar da tsaro na bayanan katin bakinka.

Idan sashen tambayoyin da ake yawan yi (FAQ) bai amsa ko daya daga tambayoyin nab a, ya y azan yi?

Idan har  amsoshin da muka samar a wannan sashe basu amsa tambayoyinka ba, ka tuntubemu ta Imel a support@allevents.ng ko kuma ka ziyarcemu a lokacin aiki (08:00 – 16:00)